Madam Largade wadda ta bayyana hakan yayin da take jawabi a taron shekara-shekara na IMF da bankin duniya, ta ce, akwai yiwuwar ci gaban tattalin arzikin duniya zai fuskanci koma baya a wannan shekara, ganin yadda ake samun mabambantan ci gaban tattalin arziki na duniya.
Sakamakon haka, asusun yana fatan rage hasashen da ya yi kan tattalin arzikin duniya a rahotonsa da yake sa ran fitarwa a taronsa na shekara-shekara a Peru cikin mako mai zuwa.
A cewar shugabar asusun na IMF tattalin arzikin kasashen da suka ci gaba zai kama hanyar bunkasa, yayin da kasashen da tattalin arkinsu ke bunkasa kuwa, za su fuskanci koma bayan tattalin arziki na shekaru biyar a jere.
A watan Yuli ne asusun na IMF ya rage hasashen da ya yi game da ci gaban tattalin arzikin duniya da kashi 0.2 cikin 100 zuwa kashi 3.3 cikin 100 inda ya yi fatan tattalin arzikin duniyan zai bunkasa da kashi 3.8 cikin a shekara mai zuwa. (Ibrahim)