in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
IMF ya rage hasashen saurin bunkasuwar tattalin arzikin duniya na bana da badi
2016-04-13 10:03:07 cri
Asusun ba da lamuni na duniya IMF ya fidda wani sabon rahoto game da hasashen saurin bunkasuwar tattalin arziki na duniya a jiya Talata 12 ga wata, inda ya bayyana cewa, yawan saurin bunkasuwar tattalin arziki na bana zai kai kashi 3.2 cikin 100, abun da ya ragu da kashi 0.2 cikin 100 bisa hasashen da ya yi a watan Janairu na bana. Ban da wannan kuma, a karkashin kokarin da gamayyar tattalin arzikin kasashe masu tasowa ke yi, an yi hasashen cewa, tattalin arzikin duniya zai karu da kashi 3.5 cikin 100 a shekara mai zuwa, amma abun da ya ragu da kashi 0.1 cikin 100 bisa hasashen da asusun ya yi a watan Janairu na bana.

Rahoton ya ce, tun daga watan Janairu na bana, kasuwar hannayen jari ta duniya ta sake shiga tangal-tangal, kuma saurin bunkasuwar gamayyar kasashe masu wadata ya ragu, kuma kasashe masu saurin bunkasuwar tattalin arziki da kasashe masu tasowa suna ci gaba da fuskantar matsin lamba. Kana, batun siyasar shiyya-shiyya da matsalar ta'addanci da 'yan gudun hijira suna ci gaba da kawo kalubale ga tattalin arzikin duniya. Bayan yin la'akari da wadannan abubuwan, IMF ya tsaida kudurin rage hasashen da ya yi game da saurin bunkasuwar tattalin arziki na bana da badi.(Bako)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China