'Yan sandan na kwantar da tarzoma za su maida hankali ne ga wanzar da tsaro a birnin na Monrovia ta hanyar gudanar da sintiri, da daukar matakan ko ta kwana tare da baiwa manyan jami'ai kariya.
Jami'an tawagar wadanda aka horas da su game da kare dokokin kasa da kasa, da amfani da makamai, sun kuma samu horo a fannin tsaron lafiyar jami'ai, tare da koyon harshen Turanci.
Tun cikin shekarar 2003 ne kasar Sin ta fara aikewa da tawagar wanzar da zaman lafiya zuwa kasar Liberia, a wani mataki na goyon baya ga shirin MDD, inda ya zuwa yanzu yawan Sinawa masu wannan aiki a kasar ta Liberiya ya kai jami'ai 500.
Liberia dai ta sha fama da rikicin siyasa tun daga shekarar 1980, lokacin da sojoji suka gudanar da juyin mulkin da ya hambarar da gwamnatin jam'iyyar True-Whing, lamarin da ya sabbaba kisan mutane kusan 250,000 zuwa 520,000, tare da gurgunta tattalin arzikin kasar. Daga bisani ne kuma aka cimma yarjejeniyar tsagaita bude wuta a shekarar 2003, tare da gudanar da zabe a shekara ta 2005. Ya zuwa yanzu kaso 85 bisa dari na 'yan kasar na rayuwa ne cikin matsi da talauci. (Saminu)