Shugaba Sirleaf wadda ta bayyana hakan cikin wata sanarwa da aka rabawa manema labarai, ta ce kayayyakin da aka kiyasce kudinsu zuwa dala miliyan uku, sun zo a dai-dai lokacin da galibin kayayyakin da sojojin kasar suke amfani da su suka lalace.
A jawabinsa jakadan kasar Sin da ke Liberiya Zhang Yue ya yaba da irin nasarorin da shugaba Sirleaf ta cimma a fannin tattalin arziki da samar da kayayyakin more rayuwa. Yana mai cewa, tallafin kayayyakin, wata alama ce da ke kara nuna imanin kasar Sin da kuma goyon bayan kokarin kasar Liberiya na tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali, a yayin da tawagar MDD da ke aikin wanzar da zaman lafiya a kasar (UNMIL) ke gudanar da aikinta da kuma jadawalin farfado da kasar bayan barkewar cutar Ebola. (Ibrahim)