Kwanan nan, shugabar kasar Liberia Ellen Johnson-Sirleaf ta furta cewa, 'yan sandan kwantar da tarzoma na kasar Sin sun ba da babbar gudummawa wajen kiyaye zaman lafiya da kwanciyar hankali a kasar Liberia, don haka ta gode musu a madadin gwamnati da kuma daukacin jama'ar kasar.
Shugaba Sirleaf ta fadi haka ne jiya Litinin a birnin Greenville, hedkwatar jihar Sinoe da ke kasar yayin da take ganawa da Zhang Guangbao, shugaban rukunin 'yan sandan kwantar da tarzoma na kasar Sin da ke Liberia.
A wannan ranar ce kuma aka shirya bikin murnar cika shekaru 168 ta samun 'yancin kan kasar Liberia a birnin Greenville, wanda ya samu halartar jami'an gwamnatin, manyan sarakunan kasar, wakilan sassan daban daban na al'ummar kasar da kuma tawagar musamman ta MDD da ke kasar ta UNMIL, gami da jakadun kasashen waje da ke kasar. Kasancewarsa rukunin 'yan sanda daya tilo da kungiyar UNMIL ta jibge a jihar Sinoe, rukunin 'yan sandan kwantar da tarzoma na kasar Sin ya dauki nauyin kiyaye tsaron jama'a a wannan rana, wanda ya samu amincewa sosai daga gwamnatin kasar Liberia da ma kungiyar UNMIL.(Kande Gao)