Shugabar kasar Ellen Johnson Sirleaf da tawagar musamamn ta MDD mai aikin wanzar da zaman lafiya a kasar Liberia wato UNMIL, da kuma jami'an jakadanci dake kasar Liberia sun halarci wannan biki.
Haka kuma, a yayin bikin, runduna daya tilo ta 'yan sandan kiyaye zaman lafiya da MDD ta aike zuwa jihar Sinoe, kana rukuni na uku na rundunar 'yan sandan kwantar da tarzoma da kasar Sin ta tura zuwa kasar, ta gudanar da ayyukan kiyaye zaman lafiya a yayin bikin yadda ya kamata.
Ayyukan rundunar dai sun hada da kiyaye tsaron manyan jami'ai, kula da aikin sufuri, kiyaye filin jirgin saman Greenville da MDD ke amfani da shi, da jiragen saman musamman na manyan jami'ai, da tankin mai da kuma wasu muhimman kayayyakin da abin ya shafa, a sa'i daya kuma, rundunar ta kula da aikin gaggawa da abin ya shafa. (Maryam)