Ana sa ran gabatar da kuduri a gun taron ministoci karo na 10 na kungiyar WTO da za a gudanar a birnin Nairobi na kasar Kenya a watan Disambar bana. Idan kasar Liberia ta cimma nasarar shiga WTO, za ta kasance kasa ta karshe a nahiyar Afirka da ta shiga WTO.
Kasar Liberia tana yammacin nahiyar Afirka, kuma tana daya daga cikin kasashe mafiya talauci a duniya. An fara yin shawarwari kan shigar da kasar Liberia a kungiyar WTO ne a shekarar 2007. (Zainab)