Kakakin MDD Stephane Dujarric wanda ya shaida hakan yayin shaidawa taron manema labarai ya ce, Mr. Zarif zai maye gurbin Karim Landgren dan kasar Sweden ne wanda aikinsa ya zo karshe a watan Yulin wannan shekara.
Kafin nadin nasa kan wannan mukami, Mr. Zarif shi ne wakilin Mr. Ban Ki-moon a kasar Kosovo kana shugaban tawagar wucin gadi ta MDD a kasar ta Kosovo(UNMIK). Bugu da kari, ya jagoranci ayyukan wanzar da zaman lafiya a kasashen Eritrea, da Liberia, da Afirka ta Kudu, da Iraki da kuma Sudan.
A shekarar 2003 ne dai aka kafa tawagar ta UNMIL wadda aka dora mata alhakin kare rayukan fararen hula da samar da agaji da kuma cimma yarjejeniyar tsagaita wude wuta, bayan yakin basasan kasar Liberiyar da ya kai ga hallaka mutane kusan 150,000, galibin su fararen hula, baya ga wasu 850,000 da suka yi gudu zuwa kasashe makabta..(Ibrahim)