Jam'iyyar ANC da ke rike da shugabancin kasar Afrika ta kudu ta yi zanga-zangar yaki da manufar wariyar launin fata a birnin Pretoria, wanda ke da nufin hada mutane 100,000 su bayyana kyamar su ga ayyukan wariyar launin fata da kuma fatansu na samun 'yancin demokuradiya na daidaici da adalci a kasar.
An fara yin zanga-zanga a wannan karo mai jigon "Hadin gwiwa da samar da dimokuradiyya, yin watsi da manufar wariyar launin fata" daga karfe 10 da safe a wannan rana, yawan mutane da suka shiga aikin ya kai dubu 87. Kuma a zangon karshen su wato fadar shugaban kasar, masu zanga-zanga sun mikawa gwamnatin kasar wata takardar shawarwari na kara karfin kafa doka, kiyaye hakkin bil Adam da dai sauransu, a cikin shawarwari kuma ana fatan mai da manufar wariyar launin fata wani laifi ne a cikin doka. Minista mai kula da harkokin mata Madam Sussan, a madadin shugaban kasar, ta karbi wannan takarda.
Jami'an ANC da fararen hula da suka shiga zanga-zanga sun bayyana cewa, burinsu ba shi da alaka da karya tsare-tsaren da ake da shi yanzu ba, a maimakon haka, ana bukatar gwamnatin da ya kyautata da daidaita su. An ce, wasu masu zanga-zanga kuma sun yi ihun "Ran Mandela ya dade, ran Zuma ya dade" don bayyana goyon bayansu ga ANC, da kuma yi suka ga jam'iyyu biyu masu adawa, wadanda ke ba da kariya ga wadanda suka aikata laifin wariyar launin fata. (Amina)