Shugaban kasar Afrika ta kudu Jacob Zuma ya gabatar da jawabi ga mahalarta taron koli na kungiyar tarrayar Afrika AU a ran 13 ga wata a birnin Johannesburg, inda ya ce, manyan sauye-sauye sun faru a Afrika a cikin shekaru da dama da suka gabata, a sa'i daya, nahiyar na fuskantar kalubaloli sosai.
A cikin jawabin nasa zuwa ga shugabannin kasashe 50 a gun taron kwamitin gudanarwa na shirin nan na NEPAD kan raya Afirka, Mr Jacob Zuma ya ce, a cikin shekaru 10 da suka gabata, shugabannin kasashen Afrika masu hangen nesa sun fito da wannan shiri, amma a cikin wani dogon lokaci, shirin ya fuskanci kalubaloli sosai saboda ganin takun-saka a siyasance, koma bayan tattalin arziki da dai sauran matsaloli da ke addabar Afirka. Amma, duk da ganin wadannan kalubaloli, Afrika na ci gaba da rike fatan na samun wadata, bunkasuwa da adalci, a haikika dai, Afrika na samun ci gaba cikin karko, kuma wasu kasashe masu saurin ci gaban tattalin arziki suna nan Afrika, haka kuma ana ta kara fid da jama'a daga kangin talauci da baiwa karin yara damar samun ilmi, baya ga haka kuma, hukumomi da tsare-tsaren dimokuradiyya na Afrika na samun ci gaba sosai, hakan ya sa ana da imani cewa, Afrika na da makoma mai haske nan gaba.
Ban da haka kuma, Jacob Zuma ya nuna cewa, ya zuwa yanzu, ana fuskantar kalubaloli masu tsanani a Afrika, daga cikinsu abu mafi tsanani shi ne rashin samun aikin yi, musamman ma a cikin matasa, matsalar da ke haifar da rashin adalci da daidaituwa a cikin dogon lokaci. Ban da haka kuma, sauyin yanayi na kawo babbar illa ga bunkasuwar Afrika mai dorewa. Ya ce, Domin cimma burin samun dauwamammen ci gaba a Afirka, ya kamata a kara mai da hankali kan gina manyan ababen more rayuwa da sa kaimi ga tsarin dunkulewar wannan yanki da yin ciniki tsakanin kasashe.
Ana kira taron koli na AU karo na 25 daga ran 14 zuwa 15 a Johannesburg, birnin mafi girma a Afrika ta kudu. (Amina)