Shugaban kasar Afrika ta kudu Jacob Zuma, ya ce ko da yake kasar sa ta samu ci gaba mai armashi a fannin shawo kan yaduwar cutar Aids ko Sida, duk da haka kamata ya yi ta kara azama, a kokarin ta na cimma burin hana yaduwar wannan mumunar cuta kafin nan da shekara ta 2030.
A cikin wani rahoto da aka fitar a ran 14 ga wata game da kandagarkin cutar ta Aids, an bayyana cewa, hukumar tsara shirin yaki da cutar Sida ta MDD, ta shigar da sunan kasar Afrika ta kudu cikin jerin kasashen da suka fi samun gaggarumin ci gaba sosai a wannan fanni.
Rahoton ya kuma bayyana cewa a cikin shekaru 10 da suka gabata, wadannan kasashe sun rage yawan mutanen su da mai yiwuwa ka iya kamuwa da cutar, da akalla kashi 20 bisa dari, kuma yawancin wadanda suka kamu da cutar a Afrika ta kudu na samun jiyya.
Bisa kididdigar da aka fitar, adadin masu ciwon SIDA da ke samun jiyya a dukkanin sassan duniya ya kai miliyan 15, inda miliyan 3.4 daga cikinsu 'yan kasar ta Afrika ta kudu ne.
Dadin dadawa, Mista Zuma ya ce, wannan rahoto ya kara masa kwarin gwiwa, wajen ci gaba da gudanar da wannan kokari. Kuma ya yi kira ga jama'ar kasar da su rika bin hanyoyin kare lafiya a harkokin su na rayuwar yau da kullum, su kuma dauki matsayin da ya dace wajen yaki da kuma rigakafin kamuwa da wannan cuta.
Kaza lika ya kuma yi kira ga jama'a da su amince da binciken lafiyar su, musamman game da cutar ta Sida, domin gano cutar tun da wuri, da kuma samun jiyya a kan lokaci. (Amina)