Gwamnatin kasar Afrika ta Kudu ta bayyana cewa, hukumar bincike laifufuka ta kasar ta fara aikin yaki da wasu laifuffuka mai lakabin "share laifuffuka", ciki hadda shiga kasar ba bisa doka ba, don tabbatar da zaman lafiya da karkon jama'arta.
Kakakin gwamnatin kasar Williams ya yi bayyani cikin wata sanarwa cewa, wannan aikin da ake yi zai kwashe makonni har ma watanni kafin a warware dukanin matsalolin da jama'arta ke fuskanta. A cewarsa, aikin ba ma kawai mai da muhimmanci kan 'yan kasashen waje ba, har ma ya mai da hankali a kan dukanin laifufuka, don tabbatar da zaman rayuwa cikin lumana na mutanen da suke zauna a kasar.
Kazalika, Mr Williams ya ce, Afrika ta Kudu wata kasa ce mai dimokuradiyya, kuma tana gudanar da ayyukan kasar bisa doka, duk wanda ke zauna a kasar, ciki hadda jama'arta da 'yan kasashen waje, za a kare su, muddin sun bi shari'ar kasar. (Amina)