A jejebirin sabuwar shekara ta 2016, shugaban kasar Afrika ta kudu Jacob Zuma ya gabatar da jawabin murnar shiga sabuwar shekarar, inda a ciki ya ce, kasar na godiya sosai ga gudunmawar da jama'arta suka bayar iri daban-daban. Afrika ta kudu tana samun ci gaba a ko wace shekara, don baiwa jama'arta zaman rayuwa mafi kyau. A ganin sa, kowa ya yi kokari cikin aikinsa a shekarar 2015, yaran talakawa da ma'aikata fiye da miliyan sun samu damar shiga makaranta, da tabbaci a fannin ingancin abinci, hakan ya sa irin wadannan yara da dama suka samun damar samun ilmi mai inganci. Ban da wannan kuma, tsoffi da talakawa suna iya zuwa asibiti lokacin da suke bukata, matakin da ya sa matsakaicin shekarun haifuwar jama'ar kasar ya karu da kashi 10 cikin dari bisa na shekaru 10 da suka gabata. Mista Zuma kuma ya kara da cewa, gwamnatin kasar na da niyyar kafa wata al'umma dake baiwa kowa zarafi na tattalin arziki, ta yadda za a kawar da talauci da rashin aikin yi, saboda hakan, a cewarsa, zai mai da hankali sosai kan gyara hanyar da kasar za ta bi ta fuskar bunkasuwar tattalin arziki a sabuwar shekara. (Amina)