Gwamnatin Afrika ta Kudu za ta yi iyakacin kokarinta domin kiyaye tsaron dukkan 'yan kasar da 'yan kasashen waje da ke cikin kasar, in ji shugabannin tawagogin diplomasiyya na kasashen Afrika a ranar Jumma'a a birnin Pretoria. Da take jawabi a gaban jami'an diplomasiyya domin yi musu bayani kan matakan da Afrika ta kudu ta dauka domin kawo karshen hare haren kyamar baki da a yanzu haka ke shafar 'yan kasashen waje dake wannan kasa, musammun ma kuma 'yan Afrika bakar fata, ministar harkokin wajen kasar Afrika ta Kudu, madam Maite Nkoana-Mashabane, ta bayyana cewa kasarta ta tsaya tsayin daka wajen kare martaba da darajar dan Adam da girmama kasa mai 'yanci. (Maman Ada)