in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Majalisar zartaswar Afrika ta Kudu ta amince da shirin Nukiliya a kasar
2015-12-25 09:44:59 cri
Majalisar Zartaswar Afrika ta Kudu ta amince da shirin kafa tashar wutar lantarki dake amfani da makamashin Nukiliya mai karfin Megawati 9,600 a kasar domin inganta harkokin lartarki.

Mai magana da yawun majalisar zartaswar Phumla Williams, shi ne ya tabbatar da hakan a jiya Alhamis.

Kasashen duniya da suka hada da Rasha, da Sin, da Faransa, da kuma Koriya ta Kudu ne suke zawarcin kwangilar aikin, wanda aka kiyasta kudinsa kimanin Rand trillion 1 kwatankwacin Dalar Amurka biliyan 70.

Bayan amincewar da majalisar ta yi, ana sa ran sashen kula da makamashin kasar zai tsara yadda za'a gabatar da neman kwangilar a nan gaba.

Gwamnatin kasar ta jima tana fafutukar yadda za'a samar da shirin makamashin Nukiliya domin magance matsalar karancin lantarki, wanda ke gurgunta shirin kayayyakin da kasar ke samarwa a cikin gida, kuma ana saran inganta lantarkin zai samar da Karin kashi 2 cikin 100 na GDP na kasar a wannan shekarar , kamar yadda bankin duniya yayi hasashe.

Wani masanin tattalin arziki Dawie Roodt, ya shedawa kamfanin dillancin labaran kasar Sin cewar, sakamakon matsalar karancin hasken wutar lantarki tun daga shekarar 2007, ya ja wa kasar hasarar sama da rand biliyan 300 kwatankwacin Dalar Amurka biliyan 20.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China