in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An hana yara nakasassu rabin miliyan shiga makarantu a Afrika ta Kudu
2015-08-19 10:33:45 cri

Rahotanni sun ce adadin yara nakasassu da ba'a ba su damar shiga makarantu a Afrika ta Kudu ba ya kai a kalla rabin miliyan.

A cewar rahoton na hadin gwiwa tsakanin hukumar kare hakkin bil adama ta Human Rights Watch da hukumar kare hakkin bil adama ta kasar Afrika ta Kudu mai shafi 94, ya bayyana karara yadda kasar Afrika ta Kudun ta ki baiwa yara nakasassu guraben shiga makarantu wadanda yawansu ya kai rabin miliyan.

Rahoton ya bayyana cewar irin wariya da kuma kyamar da ake nunawa yara masu bukata ta musamman shi ne ummal aba'isin da yayi sanadiyyar kauracewar yaran daga makarantun kasar.

Wata kwararriyar mai bincike ta sashen yara a hukumar kare hakkin dan adama ta Human Rights Watch Elin Martinez, ta ce wajibi ne a gaggauta kawar da wannan shinge domin baiwa yaran masu bukata ta musamman damar shiga makarantun kasar.( Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China