in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Jama'ar Afrika ta Kudu sun jinjinawa littafin da shugaban kasar Sin ya rubuta
2015-09-18 13:29:22 cri
Cibiyar nazarin al'adu da kimiyya ta Pretoria a Afrika ta Kudu, ta shirya wani taron nazari game da littafi mai taken tafiyar da harkokin mulki, wanda shugaban kasar Xi Jinping ya rubuta, inda manazarta a fannin siyasa da tarbiya suka jinjinawa littafin wanda ke cike da ma'ana.

A gun taron, jakadan Sin a Afrika ta Kudu Tian Xuejun, ya ce ya zuwa watan Agustar bana, yawan wannan littafi da aka bugawa a duniya ya kai miliyan 5.2, wannan baya ga kauna daga masu karatu, ya kuma shaida cewa kasashen duniya na dora muhimmanci sosai game da yanayin da Sin ke ciki, da kuma tasirin da bunkasuwar Sin zai haifar.

A nata tsokaci, mataimakiyar sakataren jam'iyyar ANC mai mulki ta Afrika ta Kudu Jessie Duarte, cewa ta yi littafi ya kunshi manufofin da shugaban Xi ya gabatar, da manyan tsare-tsaren mulkin kasar, kana ya nuna manufar samun bunkasuwar Sin da halin da take ciki.

Ta ce, a cikin littafin, manyan tsare-tsare da kuma manufar diplomasiyyar Sin, na nacewa bin hanyar samun bunkasuwa cikin lumana wadda Sin din take dauka, kuma hakan yana da ma'anar musamman ga Afrika ta Kudu. Kaza lika kuma Sin za ta yi amfani da damar da take da ita wajen samar da zarafi ga dukkanin kasashen duniya baki daya, wajen samun ci gaba, yayin da take mu'amala da kasashen duniya wajen cimma moriyar juna, Afrika ta Kudu ita ma za ta hada gwiwa da kasashen dake makwabtaka da ita domin ci gaba tare.

A nasa bangare kuma, tsohon minista a fadar shugaban kasar Essop Goolam Pahad, ya ce shugaba Xi Jinping ya yi bayanai filla-filla game da alakar dake tsakanin jam'iyyu da gwamnati da jama'a, wanda hakan ya yi matukar burge shi.(Bako)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China