Shugaban ya bayyana hakan ne jiya a gun taron koli na kungiyar AU karo na 25 da ke gudana yanzu haka a birnin Johannesburg na Afirka ta kudu.
Shugaba Zuma ya ce, al'ummar kasarsa sun nuna tsayyayiwar adawa ga nuna kyamar baki, aika-aikar da wasu tsirarrun mutane suka aikata ba zai wakilci al'ummar Afrika ta Kudu da yawansu ya kai sama da miliyan 50 ba, Afrika ta Kudu na kokarin kawo karshen yaki da aikata laifuffuka, don tsaron kasar da kare dukiyoyin jama'a.
A karshen watan Maris zuwa karshen watan Afrilun wannan shekara ce, aka samu barkewar rikicin nuna kyamar baki a biranen Johannesburg da Durban, lamarin da ya yi sanadiyyar mutuwar murtane 7, tare da jikkatar wasu sama da 100, baya ga wasu miliyoyin baki suka bar gidajensu, kana aka wawushe daruruwan shaguna na baki.(Bako)