'Yan sandan kasar Afrika ta Kudu sun cafke mutane kimanin 9.098 da ake zarginsu da aikata jerin kisan kai a wani aikin da ya shafi fadin kasar baki daya bayan tashe tashen hankalin kyamar baki na baya bayan nan. A yayin aikin mai taken Fiela da ke ma'anar kakkabe harshen sesotho, a cikin mutanen da aka cafke akwai 'yan kasashen waje, bisa alkaluman da ministan'yan sandan Nathi Nhleko ya bayar a yayin wani zaman taron 'yan majalisa.
Sai dai, mista Nhleko bai bayyana abin da ke jiran wadannan mutane da ake tsare ba ko ma bada wani karin haske kan yadda shari'arsu za ta gudana ba. (Maman Ada)