in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban kasar Afrika ta Kudu yana kan hanyar shi na halartar taron BRICS a Rasha
2015-07-08 11:14:53 cri
Shugaban kasar Afrika ta kudu Jacob Zuma yana kan hanyar sa tare da tawagar kasar domin halartar taron kungiytar BRICS karo na 7 da za'a yi a kasar Rasha,kamar yadda fadar Shugaban ta tabbatar.

Taron wanda Shugaban kasar Rasha Vladamin Putin ke daukan nauyi daga ranakun yau laraba 8 ga wata zuwa alhamis 9 ga wata zai gudana ne a birnin Ufa na kasar karkashin taken '' hadin gwiwwar BRICS, babba ginshikin cigaban duniya''.

Fadar Shugaba kasar ta Afrika ta kudu tayi bayanin cewa a wannan karon kasar ta shirya tsab ma taron.

A watan jiya majalissar dokokin kasar da majalaissar gundumomin kasar suka yi kwaskwarima game da amincewa a yarjejeniya na babban bankin raya kasar NDB, kuma duk abubuwan da zasu biyo bayan hakan an rattaba hannu a kan su.(Fatimah Jibril)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China