A yayin taron manema labarai da aka gudanar ma'aikatar kasuwancin kasar ta Sin, Mr. Shen ya bayyana ra'ayinsa dangane da wasu rade-radi dake nuna cewa farashin hajojin da ake shigo da su daga ketare zai ragu sosai, da zarar an kawo karshen wannan wa'adi na tsarin haraji, ya na mai cewa Sin ta shiga kungiyar WTO ne a ranar 11 ga watan Disambar shekarar 2001, kana ta fara rage harajin kwastan din ta daga dukkan fannoni a ran 1 ga watan Janairun shekarar 2002, inda ta gudanar da wannan aiki bisa matakai goma, kuma ta kammala galibin su a ran 1 ga watan Janairun shekarar 2005. Kaza lika ya zuwa ranar 1 ga watan Janairun shekarar 2010, kasar ta Sin ta cika alkawarin da ta dauka dangane da rage harajin kwastan, kan dukkanin hajoji.
Bisa hakan ne kuma Mr. Shen, ya ce farashin hajojin da za a shigo da su daga ketare zuwa Sin ba zai ragu sosai ba, a gabar da za a kawo karshen wa'adin tsarin kariya kan harajin kwastan a kasar ta Sin a hukunce. (Maryam)