Shugaban hukumar 'yan sanda na birnin Nairobi Japheth Koome, ya ce za a tanadi jami'an tsaro a birnin Nairobi da kewaye, sannan za'a rufe wasu tituna domin a samu damar gudanar da taron lafiya ba tare da an fuskanci matsala daga tsagerun kasar da mayakan tada kayar baya na Somali ba.
Koome, ya ce dukkanin jami'an tsaron kasar sun shirya tsab, kuma suna zaune cikin shirin ko ta kwana, don tabbatar da ganin an gudanar da taron lami lafiya.
Ya kara da cewar, za su bukaci hadin gwiwa da sauran kasashen duniya don yi aiki tare da kuma sauran jami'ai na hukumomin kula da gidan yari, da na leken asiri, na kasar Kenya domin gudanar da aikin tare.
Wannan dai shine karo na farko da za'a gudanar da taron ministocin na WTO a nahiyar Afrika, tun a shekarar 1995. Kuma ana sa ran wakilan kasashen waje dubu ne 5 zasu halarci taron.
Koome, fada a taron manema labarai cewar, za'a baza jami'an tsaron a muhimman wurare da suka hada da filin jirgin sama na Kenyatta, da hanyoyin zuwa babban dakin taro kasa da kasa na Kenyatta da otel din da za'a sauki bakin wakilai mahalarta taron. (Ahmad)