Jami'in na MDD na bayyana hakan ne a jajiberen taron ministocin karo na 10 da zai gudana daga ranar 15 zuwa 18 ga wannan wata na Disamba. Yana mai cewa, wajibi ne dokokin cinikayyar su kartata ga manufofin samar da abinci wadanda za su dace da kasashe masu tasowa, maimakon manufofin da za su rika magana kan dokokin kungiyar ta WTO kawai.
Ya ce, muddin ana bukatar samar da abinci, to, wajibi ne a gaggauta yi wa dokokin kungiyar game da aikin gona gyaran fuska. Ya kuma tunatar da mahalarta taron na birnin Nairobin Kenya game da yarjejeniyar da aka cimma tun a shekarar 2008, da kuma wadda aka cimma a Bali na kasar Indonesia a shekarar 2013 game da karancin wasu abubuwa na ci gaba, ciki har da yadda ake tafiyar da harkokin cinikayya.
A hannu guda jami'in na MDD ya nuna damuwa game da kiraye-kirayen da wasu masu shiga tsakani ke yi kan a dakatar da tattaunawar da ake kan ajandar taron Doha.(Ibrahim)