Za a yi taron ministoci na kungiyar WTO karo na 10 daga ranar 15 zuwa ranar 18 ga wannan wata a birnin Nairobi na kasar Kenya. Wannan shi ne karo na farko da aka shirya taron ministocin WTO a nahiyar Afrika.
An ba da labarin cewa, za a tattauna a kan batutuwan neman samun bunkasuwar kasashe marasa ci gaba da cinikin fitar da kayayyakin gona da kuma tsarin shawarwari na Doha, kuma za a kada kuri'u kan shigowar kasashen Laberiya da Afghanistan cikin kungiyar ta WTO.
Ministan kasuwanci na kasar Sin Gao Hucheng, zai shugabanci tawagar kasar Sin don halartar taro da kuma gabatar da jawabi.
Babban jami'in kungiyar WTO Roberto Azevedo ya bayyana cewa, a game da kasashen Afrika wadanda ke cikin jerin kasashen da suka fi koma bayan ci gaba a duniya, wannan taro na da ma'ana sosai, dole ne a cimma nasarar yin wannan taro don samun sakamako da zai kawo cin moriya ga kasashen Afrika.(Lami)