'Yan gudun hijirar Congo da ke kasar Rwanda sun yi bikin tunawa a ranar Laraba da kisan kiyashi karo na 12 da ya shafi 'yan uwansu na kabilar Tutsi da "masu sara da suka" na kabliar Interahamwe na Rwanda suka aikata tsakanin shekarar 1996 da shekarar 2004. Bikin tunawa na wannan karo ya gudana a sansanin 'yan gudun hijira na Kiziba dake shiyyar Karongi dake yammacin kasar Rwanda.
Da yake magana a yayin wannan biki, mamban kwamitin tunawa, Emile Rugari ya yi kiran 'yan kasar Congo da suka hada kansu domin jurewa rabuwar al'ummomi da kabilanci.
"Ya kamata mu yi kokarin bayyana kan mu a matsayin 'yan kasar Congo ba kawai a matsayin wasu mambobin kabilu ba", in ji Emile Rugari.
"A kasar Rwanda muke a matsayin 'yan gudun hijirar Congo, ba wai 'yan kabilar Banyamurenge, Bapfurero, Banyejomba ko wata kabilar ba. Mu hada kanmu domin komawa kasarmu", in ji mista Rugari.
Mataimakin shugaban kwamitin tunawa a cikin sansanonin 'yan gudun hijirar Congo guda biyar dake Rwanda, mista Eric Kamanzi Rusine, ya bayyana cewa, lokaci ya yi na komawa kasarsu bayan sun kwashe shekaru 19 a cikin sansanonin 'yan gudun hijira.
A nata bangare, darektar sansanin 'yan gudun hijira na Kiziba, madam Esperance Mukamusoni Kanyove, cewa ta yi, wannan aikin mayar da 'yan gudun hijira zuwa kasar su zai taimaka musu wajen samar da wani butun butumi mai kyau da 'yan uwansu da suka mutu. Wadanda suka kwanta dama an kashe su ne a cikin sansanonin wucin gadi na Mudende da Nkamira, dake yammacin Rwanda, da ke iyaka da kasar Congo. (Maman Ada)