Shugabannin kasashen Afirka sun yi shirin gudanar da wani taro nan ba da dadewa ba a wannan wata a birnin Luanda, hedkwatar kasar Angola, inda za su tattauna yadda za a kwance damarar 'yan tawayen Rwanda, wadanda suka kafa sansaninsu a gabashin kasar Congo (Kinshasa). Yanzu wa'adi ya cika da aka gindayawa 'yan tawayen da suka mika wuyansu da ajiye makamai.
Shugabannin kasashe mambobin kungiyar raya kudancin kasashen Afirka wato SADC da na kungiyar taro na yankin Great Lakes wato ICGLR za su shirya wani taro a ranar 15 zuwa 16 ga wata.
Shugabannin Afirka sun ba wa 'yan tawayen Rwanda na kungiyar FDLR wa'adi su kwance damara ko kuma su fuskanci matakin soja kansu. Wa'adin da ya cika a ranar 2 ga wata.
Tun daga watan Mayu na shekarar 2014 'yan tawaye 337 kawai suka ajiye makamai, wadanda yawansu ya kai misalin kashi 24 cikin dari bisa yawan 'yan tawayen kungiyar FDLR da aka kiyasta, in ji Jacob Zuma, shugaban kasar Afirka ta Kudu, wanda shi ne shugaban hukumar tsaro ta kungiyar SADC.
Kungiyar FDLR, kungiya ce da 'yan tawayen kabilar Hutu ta Rwanda suka kafa a gabashin kasar Congo (Kinshasa). A shekaru da dama da suka wuce, ana tuhumarsu da laifuffukan kai hare-haren ta'addanci da kuma yin kisan-kiyashi kan fararen hula. Kana kuma ana tuhumar wasu daga cikinsu da laifin kisan kare-dangi a kasar ta Rwanda a shekarar 1994. (Tasallah)