in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An kira taron kolin kasuwanci na kasashen gabashin Afirka karo na 6 a Rwanda
2014-10-17 10:55:42 cri
A jiya Alhamis ne aka kaddamar da taron kolin kasuwanci na kasashen gabashin Afirka karo na 6 a Kigali, fadar mulkin kasar Rwanda, bikin da ya samu halartar wasu jami'an gwamnati, masu zuba jari, da 'yan kasuwa na kasashen dake gabashin nahiyar Afirka.

Yayin bikin bude taron shugaban kasar Rwanda Paul Kagame ya yi kira ga kasashen da ke gabashin Afirka da su kara bude kan iyakakokin su don bunkasa harkokin cinikayya da kauran ma'aikatan kwadago tsakaninsu. A cewar shugaban, tsari na dunkule kasashe daban daban waje daya yana da amfani, ganin yadda kasar Rwanda ta samu ci gaba sosai ta wannan hanya, a shekaru 7 bayan da ta shiga kungiyar raya gabashin Afirka.

A nasa bangare, shugaban kasar Kenya Uhuru Kenyatta ya bayyana ra'ayinsa cewa, wasu mutane suna shakka kan tsarin dunkulewar kasashen waje guda, wai da sunan suna kare moriyar kasashensu, amma a hakika an kafa kawancen kayyade harajin kwastam da kasuwar bai daya ne bisa wannan tsari, ta yadda za kara cin gajiyar cinikayya da aikin zuba jari sosai. A cewar shugaban, ya zuwa yanzu an samu ci gaba sosai a wannan fanni, amma ana bukatar kara bude kofa.

Za a yi kwanaki 2 ana gudanar da taron, wanda ke da jigon 'ci gaban tattalin arzikin yankin da samun karuwar da za ta kunshi bangarori daban daban'. (Bello Wang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China