Faransa da Amurka na daga cikin kasashen da ake zargi da karbar masu tunanin kisan kare dangi a cikin kasashensu, har da ma 'yan asilin Faransa da masu bincike 'yan Amurka sunayensu na kasancewa cikin wani fim din da aka tsara mai cike sarkakiya mai taken "Rwanda's Untold Story".
Wannan fim ya kai ga tilastwa Kigali dakatar a ranar 29 ga watan Mayu, da shirye shirye a cikin harshen gida na BBC a cikin kasar Rwanda.
Kwamitin kasa na yaki da kisan kare dangi (CNLG) ya bayyana cewa ana kara samun tunanin shakkun kisan kare dangi a yayin binciken tunawa da kisan kare dangi karo na 21 a kasar Rwanda.
Da yake magana gaban 'yan jarida a ranar Jumma'a a birnin Kigali domin gabatar da wani rahoto kan bikin tunawa na wannan shekara, dokta Jean Damascene Bizimana, babban sakataren kwamitin CNLG, ya bayyana cewa an gano nau'in shakkun kisan kare dangi 168, idan aka kwatanta da na shekarar bara da ke 86.
Ya bayyana cewa wannan karuwa na dalilin cewa bukukuwan tunawa an shirya su a cikin kauyuka. (Maman Ada)