A cewar ma'aikatar dake kula harkokin 'yan gudun hijiri da bala'u, yawan 'yan gudun hijirar Burundi dake kasar Rwanda ya cimma dubu 6.571 a ranar Laraba da yamma, idan aka kwatanta da na dubu hudu a makon da ya gabata, kuma yawancinsu yara kanana ne. Mista Antoine Ruvebana, sakataren dindindin a ma'aikatar kula da 'yan gudun hijira da bala'u, ya bayyana wa manema labarai a ranar Jumma'a cewa adadin na ci gaba da karuwa. (Maman Ada)