Masu zuba jarin su sama da 30 karkashin jagorancin shugaban cibiyar cinikayyar kasar Sin a gabashin Afirka Han Jun, sun bayyana wannan matsayi na su ne a birnin Kigali, inda suka ce za su duba yiwuwar shiga harkokin gina ababen more rayuwa, da harkar masana'antu, da kuma ta gine-ginen gidaje.
A cewar shugaban tawagar, matakin da cibiyar ta sa za ta dauka zai taimaka wajen janyo hankalin karin Sinawa su zuba jari a Rwanda, da ma sauran sassan yankin na gabashin Afirka.
Da yake maida jawabi yayin ganawar sa da tawagar 'yan kasuwar, shugaban ofishin samar da ci gaba na kasar ta Rwanda Francis Gatare, cewa ya yi tawagar daya ce daga matakan da ake dauka, na janyo Sinawa masu zuba jari kasar ta Rwanda.
A yanzu haka dai yawan jarin da Sinawa masu zuba jari ke da shi a Rwanda cikin shekaru 5 din baya bayan nan, ya haura dalar Amurka miliyan 170. Adadin da ya hada da kudaden cinikayyar shige-da-fice tsakanin kasashen 2. (Saminu Alhassan)