Mr Ban ya ce an dauki darussa daga mawuyacin halin da aka shiga na tashin hankalin da aka fuskanta a kasar Rwanda lokacin da aka yi kisan kare dangi a shekarar ta 1994, kuma an amince ga baki daya cewa hakan ba zai sake faruwa ba, sai dai abin bakin ciki shi ne shekara daya da wannan sai na Srebrenica ya auku don haka ya zama dole a hana faruwan irin wadannan ayyukan kisan kare dangi.
Magatakardar daga nan sai ya yaba ma kasar ta Rwanda bisa ga kokarin ta wajen samar da zaman lafiya a kasar Sudan ta kudu wanda ita ke da adadi mafi yawa a sojojin kiyaye zaman lafiya da MDD ta tura.
A nashi bangaren shugaba Paul Kagame na Rwandan ya ce halarta Magatakardar MDD da kan shi a kasar Rwanda domin tunawa da wadanda suka rasu a kisan kare dangin shekaru 20 da suka gabata wani alamu ne na irin goyon bayan da MDD take nuna ma kasar bayan aukuwar wannan tashin hankali a tarihi.
Mr. Ban dai ya je kasar Rwanda sau da dama kafin haka, amma a cewar Shugaban Kagame, wannan ziyarar ta banbanta da sauran kuma tana da matukar muhimmancin gaske. (Fatimah)