Kaberuka ya bayyana hakan ne jiya Litinin a nan birnin Beijing, a gun taron tattaunawa wanda kasar Sin da hukumar CCG suka dauki bakunci, a ci gaba da ziyarar aiki da yake gudanarwa a nan kasar Sin.
Bugu da kari Kaberuka ya bayyana cewa, AIIB ya kasance misali ga sabbin hukumomin hada-hadar kudi na karni na 21, yana kuma fatan zai gana da jami'an AIIB a ranar 21 ga wata. A ganinsa, adadin jarin da ake bukata a zuba ga kasashen duniya, musamman ma nahiyar Afirka yana da yawa, kuma a matsayin sabuwar mamba a hukumar raya kasa da hada-hadar kudi ta duniya, bankin AIIB zai ba da damar samar da hanyar tattara kudi domin gina ababen more rayuwa.
A farkon watan Yulin bana ne dai cikin wata haddadiyar sanarwa, AFDB, da bankin duniya, da asusun ba da lamuni na duniya da sauran hukumomin hada-hadar kudi na duniya suka bayyana cewa, ayyukan taimakawa kasashe mafiya talauci da yawansu ya kai dala biliyan 135 bai kai ga cimma nasarar da ake fata ba. Kuma bukatun tattara kudi a fannin ayyukan more rayuwa na kasashe masu tasowa, da sabbin kasashe mafiya samun bunkasuwar tatalin arziki a kowace shekara, ya kai dala biliyan 1500.
Game da hakan, Kaberuka ya ce, yanzu haka yawan jarin da ake bukata don gina ababen more rayuwa a nahiyar Afirka a kowace shekara, ya kai dala biliyan 50, kuma AFDB na fatan dagewa tare da AIIB, wajen sa kaimi ga gina ababen more rayuwa a nahiyar Afirka. (Zainab)