Kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Lu Kang ya sanar a yau cewa, za a fara tarukan kulla yarjejeniyar bankin zuba jari kan kayayyakin more rayuwa na Asiya, watau AIIB a ran 29 ga wata a birnin Beijing. Kuma a yayin tarukan, shugaban kasar Sin Xi Jinping zai gana da shugabannin tawagogin wakilan mambobin kasashen dake son kafa bankin AIIB, kana firaministan kasar Sin Li Keqiang zai gabatar da wani jawabi a rubuce ga ministocin kudi na kasashe masu son kafa bankin AIIB.
Ya zuwa ranar 31 ga watan Maris na bana, mambobin kasashen dake son kafa bankin AIIB ya karu zuwa guda 57, kuma mambobin sun fito ne daga manyan nahiyoyi guda biyar da suka hada da Asiya, Oceania, Turai, Latin Amurka da kuma Afirka, lamarin da ya sa, bankin ke da wakilci a duniya. (Maryam)