A jawabinta, shugabar IMF Christine Lagarde ta ce, bankin AIIB wata hukuma ce da za ta dukufa ka'in da na'in game da raya muhimman ababen more rayuwa na shiyya-shiyya kawai, abin da ya jawo hankalin hukumomi daban daban na duniya, ciki har da IMF,wadda take maraba da kafa bankin AIIB kuma za ta ci gaba da hadin gwiwa da shi.
A nasa bangare kuma, a gun taron manema labaru da aka shirya a jiya, shugaban bankin duniya Jim Yong Kim ba ma kawai ya yi maraba da kafa bankin AIIB ba, hatta ma ya bayyana hanyoyin da bangarorin biyu za su bi don hadin gwiwa a tsakaninsu. Kazalika ma, ya ce, sabo da ana matakin kafa bankin AIIB, don haka bankin duniya na da kwararru da yawa fiye da na bankin AIIB na yanzu, shi ya sa yana fatan ganin kwararrun za su taimakawa bankin AIIB a fannin gudanar da wasu ayyuka.(Bako)