A cikin sakonsa, Mr Li ya bayyana cewa, daga cikin kasashe 57 da suka kokarta kafa bankin AIIB, akwai kasashe masu tasowa, akwai kuma masu karfin tattalin arziki har ma da masu sukuni, shi ya sa suke iya wakiltar sassa daban daban tare da ba da babban tasiri. Ya lura da cewa gudanar da hadin gwiwa tsakanin wadannan kasashe wajen raya manyan kayayyakin more rayuwa da sauransu zai taka muhimmiyar rawa wajen farfado da tattalin arzikin duniya. Firaministan na Sin yace kafuwar bankin AIIB za ta ba da gudummawa wajen fadada hanyar tattara kudi ga raya manyan kayayyakin more rayuwa.
A don haka Mr Li ya jaddada cewa, Sin na fatan sa kaimi ga yin mu'amala tsakanin bankin AIIB da sauran hukumomi bisa ka'idar bude kofa ga kasashen waje da yin hakuri da kuma sa haske a ciki, a cewar sa duk wannan a kokarin kafa manyan kayayyakin amfanin jama'a da yin mu'amala da juna yadda ya kamata. Daga nan sai yayi fatan bangarorin daban daban zasu yi amfani da wannan dama, su kara fidda manufofin kyautatuwa daga manyan fannoni, a kokarin yin hakikanin hadin gwiwa da samun moriyar juna, ta yadda za a sa kaimi ga samun farfadowar tattalin arziki da karuwar sa a duniya baki daya.(Fatima)