Wakilin kasar Sin kan daddale yarjejeniyar kana ministan kudin kasar Sin Lou Jiwei ya rattaba hannu kan shirin, sannan ya yi jawabin fatan alheri, inda ya ce, dalilin da ya sa Sin ta yi kokarin tabbatar da kafuwar bankin AIIB shi ne, don kara daukar alhakin da ke kanta na raya tattalin arziki a kasashen Asiya da duniya baki daya, da sa kaimi ga samun moriyar juna da samun nasara tare. Matakan da Sin ta dauka za su kawo moriya ga kasashe daban daban, kana sun samu karbuwa daga bangarorin da abun ya shafa.
Mista Lou ya ce, bikin rattaba hannun ya kasance wani babban mataki na yunkurin kafa bankin AIIB, lamarin da ke nuna cewa, yarjejeniyar kafa bankin ta samu amincewa daga dukkan fannoni.
Bisa abubuwan da aka tanada cikin yarjejeniyar, kasashen dake da niyyar shiga bankin AIIB, amma ba su daddale yarjejeniya a wannan karo ba, za su kammala rattaba hannu kafin karshen shekarar bana.(Bako)