Muna aiki tare da kasashen Asiya domin tabbatar da ganin cewa jarin AIIB ya amfana wa kasashen Afrika, in ji mista Kaberuka a yayin wata hira tare da kamfanin dillancin labarai na Xinhua dake birnin Nairobi a ranar Alhamis.
Kasar Sin ta shawarta kafa bankin AIIB a shekarar 2014 bisa burin samar da kukaden gina ababen more rayuwa a cikin kasashen da basu da karfin samun irin wadannan kudade na yin irin wadannan manyan ayyuka. Ya zuwa yanzu, kasashe 57 suka bayyana niyyarsu na kasancewa mambobi a cikin bankin AIIB, wadanda suka hada da mambobin kungiyar G7 kamar Burtaniya, Jamus, Faransa da Italiya.
Bankin zai tanadi kudin gudanarwa da aka amince na dalar Amurka biliyan 100, kana kudin ajiya na farko zai tashi zuwa dalar Amurka biliyan 50.
Wakilan kasashe 57 da ake tsammanin zasu kafa bankin AIIB zasu sanya hannu a ranar Litinin mai zuwa a birnin Beijing, kan kundin da ke samar da tsarin dokokin kafa wannan babbar hukumar kudi ta duniya. (Maman Ada)