in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Manzon musamman ta shugaban Sin ta halarci bikin rantsar da shugaban Mozambique
2015-01-16 20:30:58 cri
Bisa gayyatar da kasar Mozambique ta yi wa kasar Sin, Manzon musamman ta shugaban kasar Sin, kana ministar kula da harkokin shari'a ta Sin Wu Aiying ta halarci bikin rantsar da sabon shugaban kasar Mozambique Filipe Nyusi, da aka yi a birnin Maputo, a jiya Alhamis 15 ga wata, kana a yau ta gana da shugaba Nyusi .

A yayin ganawarsu, Wu Aiying ta taya wa shugaba Nyusi murna tare da yi masa kyakyyawar fata a madadin shugaban kasar Sin Xi Jinping, ta ce, kasar Sin tana son kara inganta huldar siyasar dake tsakaninta da kasar Mozambique tare da karfafa hadin gwiwar kasashen biyu cikin harkokin kasa da kasa, domin ciyar da zumuncin kasashen biyu gaba.

A nasa bangaren, shugaba Nyusi ya nuna yabo sosai kan dangantakar dake tsakanin kasarsa da kasar Sin, ya kuma nuna godiya ga kasar Sin dangane da taimako da goyon baya da take baiwa kasarsa cikin dogon lokaci. Ya ce, yana fatan za a ci gaba da inganta hadin gwiwar dake tsakanin kasashen biyu a fannoni daban daban. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China