Maiteeq ya bayyana a birnin Tripoli a wannan rana cewa, bayan da ya tattauna da tawagar mashawarta, ya tsaida kudurin sake shiga takara a zaben firaministan gwamnatin wucin gadi ta kasar da za a yi bayan da aka kafa majalisar wakilan jama'ar kasar.
Ban da wannan kuma, Maiteeq ya ce, ana bukatar sabbin shugabanni a kasar Libya, kuma tawagarsa tana da kwarewa da karfin jagorancin kasar har ma da magance matsalolin siyasa da tattalin arziki da kasar ke fuskanta.
Majalisar wakilan jama'ar kasar Libya ce za ta zabi sabon firaministan gwamnatin wucin gadin kasar. An gudanar da zaben majalisar wakilan jama'ar kasar a ranar 25 ga watan Yuni, ana sa ran cewa, za a gabatar da sakamakon zaben a ranar 20 ga wannan wata. (Zainab)