Ministocin harkokin wajen kasashen Algeria, Masar, Sudan da kuma Tunisia sun yi shawarwari kan yanayin kasar Libya a yayin da suka halarci taron ministoci karo na 17 na kungiyar kasashe 'yan ba ruwanmu. A yayin ganawar tasu, ministocin kasashen hudu sun cimma matsaya guda wajen sa kaimi ga bangarorin da abin ya shafa na kasar Libya da su yi shawarwarin a duk fadin kasar, da kuma kiyaye yanayin zaman karkon kasar tun bayan kifar da gwamnatin Mohamar Kaddafi, bugu da kari, sun kuma yi kira ga bangarorin da abin ya shafa da su girmama hukumomin kasar, ciyar da yunkurin dimokuradiyya gaba cikin yanayin zaman lafiya da na zaman karko. (Maryam)