in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Babban magatakardar MDD ya damu matuka da halin da ake ciki a kasar Libya
2014-05-25 15:40:08 cri
Babban magatakardar MDD Ban Ki-Moon, ya bayyana damuwar sa game da yadda al'amura ke dada tabarbarewa a kasar Libiya, musamman ma kan batun yaduwar ayyukan soji a ciki da wajen birnin Tripoli, fadar gwamnatin kasar.

Cikin wata sanarwar da kakakin sa ya fitar, Mr. Ban Ki-Moon ya yi kira ga daukacin masu fada a ji a kasar, da su koma teburin shawara, domin kawo karshen halin rashin tabbas da kasar ke fuskanta.

Kaza lika babban sakataren MDDr ya ja hankalin masu ruwa da tsaki, da kuma tsagin mahukunta, da su sauke nauyin da ke wuyan su, na kiyaye doka da oda tare da baiwa fafaren hula cikakkiyar kariya.(Saminu Alhassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China