Libya ta nuna rashin dadinta ga Amurka bisa kama mutumin da ake zargi da hannun kai hari ga ofishin jakadancinta dake Benghazi
Ministan shari'ar kasar Libya Salah Magani ya gudanar da taron manema labaru a ranar 18 ga wata a madadin gwamnatin wucin gadi ta kasar, inda ya yi tir da matakin soja na musamman na kasar Amurka ta dauka wajen kama Ahmed Abu Khatallah da ake zargi da hannun kai harin ofishin jakadancin kasar Amurka dake birnin Benghazi, kana ya bukaci kasar Amurka da ya mika wannan mutum ga Libya.
Magani ya bayyana a gun taron manema labaru cewa, kasar Amurka ba ta sanar da bangaren Libya wajen kama wannan mutumin ba, don haka wannan aiki ya keta ikon mallakar kasar Libya.
Kakakin ma'aikatar wajen kasar Libya ya bayyana cewa, aikin kama Khtallah da kasar Amurka ta yi ya keta ikon mallakar kasar Libya, kuma kasar Libya tana da ikon yanke hukunci ga Khtallah bisa dokar kasar. (Zainab)