in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An kammala jefa kuri'u a zaben majalisar wakilan jama'ar kasar Libya
2014-06-26 14:37:52 cri
A ranar 25 ga wata da karfe 8 na yamma bisa agogon wurin, hukumar gudanar da zaben kasar Libya ta ce, an kammala jefa kuri'u a zaben majalisar wakilan jama'ar kasar da ta gudanar a Libya, inda kuma ake fatan fara kidaya su ba tare da bata lokaci ba.

A cewar hukumar, bisa kididdigar da aka gudanar, yawan kuri'un da aka kada a zaben na wannan karo ya kai kashi 45 cikin dari.

Wani jami'in hukumar ya bayyanawa wani taron manema labaru cewa, an kai hare-hare wasu tasoshin jefa kuri'un zaben guda 8, lamarin da ya haddasa rufe wasu tasoshin zaben a dab da wurin da hare-haren suka auku.

Kaza lika ya bayyana cewa sakamkon matsanancin hali da ake ciki a kasar, akwai yiwuwar a amince da kashi 45 cikin dari, na yawan kuri'un da aka jefa. Koda yake bai bayyana yaushe ne za a sanar da sakamakon zaben ba. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China