in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Firaministan wucin gadi a Libiya ya ki mika mulki ga sabuwar gwamnatin wucin gadin kasar
2014-05-29 11:06:31 cri
Firaminista mai barin gado a gwamnatin wucin gadin kasar Libya Abdullah al-Thinni, ya bayyana rashin amincewarsa da mika mulkin kasar ga sabon jagoran gwamnatin wucin gadi Ahmed Maiteeq.

Al-Thanni wanda ya bayyana hakan yayin wani taron manema labarai da ya gudanar a jiya laraba, ya ce bayanai game da zaben Ahmed Maiteeq da ya samu daga majalissar dokokin kasar ta Libiya na cin karo da juna. Don haka ya ayyana kudurinsa na ci gaba da jagorantar gwamnatin wucin gadin kasar, har sai majalisar dokokin kasar ta tantance batu kan hakan.

Rahotanni dai sun ce Ahmed Maiteeq ya lashe zaben firaministan gwamantin Libiyan ne, sakamakon goyon bayan da ya samu daga kungiyoyin masu ra'ayin addini a ranar 4 ga watan nan na Mayu. Ko da yake dai sai da aka kai ga zagaye na biyu na zaben da majalissar ta kada, kafin ya kai ga samun kuri'u 121, da ake bukata. Hakan ne dai ya sanya ya zuwa yanzu wasu ke takaddama kan lashe zaben da ya yi.

Bugu da kari a ranar 5 ga watan nan, shugaban majalisar dokokin kasar Nuri Abu Sahmain, ya sa hannu kan takardar amince da Ahmed Maiteeq, a matsayin sabon firaministan gwamnatin wucin gadin kasar, an kuma riga an rantsar da sabuwar gwamnatin karkashin jagorancin Ahmed Maiteeq a ran 26 ga watan. Kafin daga bisani babban mataimakin shugaban majalisar dokokin kasar Ezzedin al-Awami, ya bayyana kin amincewarsa da halascin zaben Ahmed Maiteeq, bisa zargin cewar bai kai ga samun isassun kuri'un da aka tsara cikin dokar zaben kasar ba. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China