Bisa labaran da aka samu daga kafofin watsa labaran kasar Libya, an ce, makarantu da dama a wurin sun dakatar da koyarwa, wasu kantuna su ma sun rufe shagunansu, sannan an rufe hanyar zuwa filin jirgin sama don haka an dakatar da fasinjoji da dama a filin jirgin sama domin rufe filin da yajin aiki ya haddasa, kuma wasu jiragen sama wadanda suke niyyar sauka a birnin Benghazi sun koma inda suka fito.
Yanayin tsaron kasar Libya na ci gaba da tada hankulan jama'ar kasa bayan yakin kasa, musamman ma a birnin Benghazi. Cikin shekara daya daya gabata, an sha fama da kisan gillar sojoji da kuma masu kiyaye tsaron yankin a birnin Benghazi, har ma an yi kashe tare da yin garkuwa da wasu fararen hula. (Maryam)