A cikin makwanni biyu da suka gabata, an samu mummunan rikici a garin Sabha da ke yankin kudancin kasar Libya, ya zuwa ranar 25 ga wata, lamarin da ya haddasa mutuwar mutane a kalla 88, tare da jikkatar wasu 130.
Shugaban asibitin Sabha Abdullah Wahida ya fayyace cewa, wannan adadi ba ya kunshe da yawan mutanen da suka rasu yayin rikicin da ba a kai su asibitin ba.A ranar 11 ga wata, an samu rikicin kabilanci a yankin Sabha da ke da nisan kilomita 800 da babban birnin kasar Libya, lamarin da ya haddasa mutuwar mutane sama da 10, har yanzu kuma ana cigaba da samun a wannan yanki.
A ranar 18 ga wata, dakarun dauke da makamai sun kai hari a wani sansanin sojojin sama da ke kusa da Sabha. A halin yanzu, firaministan gwamnatin wucin gadi ta Libya Ali Zeidan ya amince da cewa, halin tsaro da ake ciki a Sabha ya sake tsananta. (Bako)