Sanarwar ta ce, a cikin shekarar 2013, aikin tsaron jama'a a kasar Libya ya fuskanci matsala sosai, kuma kisan gilla, da rikicin da ke tsakanin dakaru daban daban, da harin bama-bamai sun zama manyan musabbabin da suka haddasa mutuwar mutane a kasar. Ko da yake,yanzu akwai 'yan sanda da yawansu ya kai dubu 250 a kasar, amma ba a cimma nasarar tattara makamai da ke hannun fararen hula a kasar ba, kuma adadin 'yan sanda ba su da yawa in an kwatanta su da yawan al'ummar kasar.
Tun daga ranar 22 ga wata, ake ci gaba da fuskantar rikici a yankin Wershefana da ke yammacin birnin Tripoli hedkwatar kasar Libya, da Sabha da ke kudancin kasar, rikicin da ya haddasa mutuwar mutane sama da 30, tare da jikkata wasu kimanin 100.(Bako)