Gwamnatin wucin gadi ta ce, a baya dai an ba da umurni ga duk dakarun jama'a da su janye jiki daga babban birnin kasar kafin ran 20 ga wata, kuma dakarun jama'a na Misurata da suka mamaye babban birnin ba bisa doka ba.
Yanzu, an rufe duk shagunan dake birnin Tripoli, kuma jama'a suna adawa ga dakarun da suka yi kisan jama'a da mamaye birnin ba bisa doka ba.
A ranar 15 ga wata, dakarun dauke da makamai na Misurata sun harbi bindiga ga jama'a da ke yankin Galgul. Ma'aikatar kula da harkokin kiwon lafiya ta bayyana cewa, abin da ya yi sanadiyyar mutuwar mutane 43, tare da jikkatar wasu 460.(Bako)