Yayin da kakakin dakarun Renamo ke zantawa da manema labaru, ya zargi jam'iyya mai mulki wato Partido Frelimo da cewar ta kwace albarkatun kasar, sannan tana matsin lamba ga jam'iyyar adawa.
A daren ranar 4 ga wata, fadar shugaban kasar Mozambique ta ba da wata sanarwa, inda ta ce, shugaban kasar Armando Emílio Guebuza ya gayyaci jagoran jam'iyyar Renamo Afonso Dhlakama da ya zo domin yin shawarwari kai tsaye a tsakaninsu biyu a birnin Maputo a ranar 8 ga wata, don sassauta halin kunci game da harkokin siyasa a kasar. Haka kuma, a cikin sanarwar, an ce, shugaba Guebuza yana fatan yin shawarwari don warware rikici a tsakaninsu.(Bako)