Fadar shugaban kasar Faransa da ma'aikatar harkokin wajen kasar sun ba da sanarwar yin Allah wadai da harin da aka kai. Tuni shugaban kasar François Hollande ya umurci ma'aikatar harkokin wajen kasar da ta tura jami'i zuwa wurin tare da daukar duk wani matakin da ya wajaba ta yadda za a dawo da 'yan Faransa biyu da suka raunata gida. A sa'i daya kuma, gwamnatin kasar Faransa ta kalubalanci mahukuntan kasar Libya da su yi cikakken bincike kan lamarin tare da gurfanar da wadanda suka aikata laifin a gaban koku.
Ban da haka, firaministan kasar Faransa Jean-Marc Ayrault ya sheda a wannan rana cewa, kawo yanzu babu wata kungiya ko wani mutum da ya sanar da daukar alhakin kai wannan hari.
Dadin dadawa, kwamitin sulhu na MDD da kuma babban sakataren majalisar Ban Ki-Moon sun ba da sanarwa daya a wannan rana, inda suka yi tir da harin da aka kai tare kuma da nuna juyayi ga iyalan wadanda harin ya shafa. (Amina)